15 Yuni 2025 - 00:00
Source: ABNA24
Iran Ta Harba Guguwar makamai masu linzami a wuraren Isra'ila A Daren Nan

Iran Ta sake kai wa yankunan da Isra’ila hari da daruruwan makamai masu linzami a daren nan.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti ta kasa da kasa ABNA ya bayar da rahoton cewa: kafar yada labarai ta yahudawa sun rawaito cewa, ana ci gaba da harba makami mai linzami daga kasar Iran zuwa yankunan da aka mamaye.

A bisa wanna rahoton an harba makamai masu linzami daga sassa daban-daban na Iran kamar Tehran Shiraz zuwa sassa daban-daban na matsugunan yahudawan sahyoniya a kasar Isra'ila.

Bayan wannan harin makami mai linzami mai yawan gaske an yi ta jin ƙarar ƙararrawar kowa yayi ta kansa a cikin yankunan da aka mamaye.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha